Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin masu harbuwa da COVID-19 a Najeriya na raguwa
2020-08-11 19:44:56        cri
Babban jami'in tsare-tsare a kwamitin da fadar shugaban Najeriya ya kafa, domin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 ko PTF a takaice Sani Aliyu, ya ce adadin masu harbuwa da wannan cuta na ci gaba da raguwa, inda adadin masu kamuwa da ita a kullum tun daga karshen watan Yuli da ya shude zuwa yanzu, ba ya wuce kusan mutum 400, adadin da ya yi kasa da na farko-farkon watan Yuni, zuwa karshen watan Yuli, wanda a wancan lokacin ya rika kaiwa kimanin sama da mutane 500 a kullum.

Cikin wata sanarwa da jami'in ya fitar, wadda kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafi, ya ce hakan ba wai yana nuna an cimma nasara gaba daya ba ne, don haka ya zama wajibi a ci gaba da aiwatar da matakan kandagarki da ba su shafi shan magani ba, har a kai ga kawar da cutar ta COVID-19 daga sassan Najeriya baki daya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China