Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan wadanda suka kamu da COVID-19 a Afirka ya zarce miliyan 1.05
2020-08-12 10:34:15        cri

Cibiyar kandagarki da hana yaduwar cututtuka ta Afirka (Africa CDC) ta bayyana jiya Talata cewa, yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a nahiyar, ya karu zuwa 1,055,964, yayin da yawan wadanda cutar ta halaka ya karu zuwa dubu 23,582, kana ya zuwa yanzu mutane 744,438 sun warke daga cutar.

Har yanzu dai kasar Afirka ta kudu ce ke kan gaba, wajen yawan masu fama da cutar da suka kai 563,598 da ma wadanda cutar ta halaka ta yawansu ya kai 10,621.

Kasar Masar ke bi mata baya da mutane 95,666 da suka kamu da cutar, sai mutane 5,035 da suka mutu sanadiyar cutar, yayin cutar ta kama mutane 46,867 a Najeriya, ta kuma halaka mutane 950 a kasar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China