2020-08-13 09:38:55 cri |
Rahotanni daga Najeriya na tabbatar da cewa, ministan harkokin wajen kasar Geoffrey Onyeama, ya warke daga cutar numfashi ta COVID-19, bayan kebe kansa na makonni uku.
Ministan wanda aka tabbatar ya kamu da cutar a ranar 19 ga watan Yulin da ya gabata, ya wallafa a shafinsa na twita cewa, sakamakon gwaji na baya-bayan aka yi masa bayan killace kansa na tsawon makonni uku, ya nuna cewa, ya warke daga cutar.
A don haka kamar yadda waccar kafa a baya ta sanar da cewa, ya kamu da cutar COVID-19 a watan da ya gabata, yanzu ba ya dauke da kwayar cutar. (Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China