Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Afrika ta kudu ta shirya yiwuwar sake yaduwar cutar COVID-19
2020-08-15 16:01:17        cri
Ministan lafiyar kasar Afrika ta kudu Zweli Mkhize, ya sanar a ranar Juma'a cewa, kasar ta sake yin shiri na yiwuwar sake bazuwar annobar COVID-19, wacce aka fara ganin alamun raguwarta a 'yan kwanakin nan.

Afrika ta kudu ce inda annobar COVID-19 ta fi kamari a nahiyar Afrika, inda take da sama da rabin yawan mutanen da suka kamu da cutar a nahiyar.

A duk duniya, kasar ce ke mataki na biyar na yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar, baya ga Amurka, Brazil, Indiya da Rasha.

Da yake maida martani game da kiraye kirayen da ake yi na nema a sassauta dokar kullen da aka sanya a kasar domin bada damar sake bude harkokin kasuwanci da tattalin arzikin kasar, Mkhize ya ce, har yanzu gwamnatin kasar ba ta cimma matsaya game da ko za ta saukaka dokokin kulle da aka kakabawa kasar ba.

A cewar ministan, har yanzu batun yana gaban kwamitin yaki da annobar COVID-19 na kasar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China