Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ghana ta fidda jadawalin babban zaben kasar na watan Disamba
2020-08-15 16:02:25        cri
Hukumar zaben kasar Ghana EC, ta fitar da jadawalin babban zaben kasar dake tafe a watan Disamba, bayan kammala aikin rejistar masu zabe, kamar yadda hukumar ta wallafa a shafinta na intanet ranar Juma'a.

Hukumar ta tsara 5 ga watan Oktoba a matsayin ranar zaben fidda gwani na 'yan takarar shugabancin kasa da na 'yan majalisun dokokin kasar.

EC ta kara da cewa, za ta kammala aikin rarraba sunayen masu zabe da aka tantance ga dukkan jam'iyyun siyasar kasar a ranar 6 ga watan Nuwamba.

Za a fara babban zaben na shekarar 2020 a ranar 1 ga watan Disamba, inda za'a baiwa jami'ai na musamman damar jefa kuri'un su da suka hada da jami'an tsaro, 'yan jarida, da sauran jami'an kungiyoyi daban daban wadanda ba za su iya samun damar zuwa rumfunan zabensu ba a ranar zaben saboda yanayin aikinsu. Sauran jama'a za su kada kuri'unsu a ranar 7 ga watan Disamba, inda za'a bayyana sakamakon zaben zuwa ranar 10 ga watan Disamba.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China