Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta tura dakaru don magance matsalar tsaro a arewacin kasar
2020-08-15 20:35:10        cri
Helkwatar rundunar tsaron Najeriya ta amince ta tura tawagar dakarun tsaro na musamman domin magance matsalar tsaro dake addabar shiyyar kudancin jahar Kaduna, gwamnan jahar Nasir El-Rufai ya sanar da hakan.

Ya zuwa yanzu tawagar dakarun tsaron ta musamman da aka zabo daga rundunar sojojin kasar ta riga ta isa yankin Kafanchan, a karamar hukumar Jema'a dake jahar ta shiyyar arewacin kasar tun a ranar Juma'a, yankin dai ya shafe shekaru yana fama da matsalolin yawaitar hare-hare wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar fararen hula masu yawa.

A sanarwar da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a yau Asabar, gwamna El-Rufai ya bayyana kyakkyawar fata cewa, tawagar dakarun tsaron ta musamman da aka tura zuwa yankin kudancin Kaduna za ta magance kalubalolin tsaro dake damun shiyyar.

Gwamnan ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da baiwa fannin tsaro fifiko kasancewar shi ne kashin bayan duk wani ci gaba mai dorewa.

Tun da farko a ranar Juma'a, John Enenche, kakakin rundunar tsaron Najeriya ya ce, ana fatan wannan yunkuri zai samar da kyakkyawan sakamakon da ake bukata sakamakon aikin magance matsalar tsaron da aka shirya tun daga tushe. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China