Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumomin Algeria sun bukaci jama'a su kiyaye dokokin yaki da COVID-19 bayan sake bude masallatai a kasar
2020-08-16 16:59:08        cri
Ministan al'amurran addinai na kasar Algeria Youcef Belmahdi, a ranar Asabar ya bayyana cewa, mutunta dokoki da matakan kiwon lafiya na kandagarkin annobar COVID-19 su ne za su tabbatar da dorewar cigaban sake bude masallatan kasar.

Kamfanin dillancin labarai na APS ne ya bada rahoton, inda ya ce, ministan yayi wannan tsokaci ne a lokacin ziyarar da ya kai zuwa wani mallacin kasar a ranar Asabar bayan da gwamnatin kasar ta bada umarnin sake bude wasu daga cikin masallatan kasar, da wuraren shakatawa, da na wasanni.

Ya bukaci dukkan jama'ar kasar da su kiyaye dokokin kandagarkin annobar, inda yayi maraba da dukkan halayya ta gari da mutane ke nunawa a lokacin da suke gudanar da ibadun a sassan kasar, musamman na rashin yin sakaci da matakan kula da tsafta.

Gwamnatin Algeria ta bude masallatai 1,000 a ranar Asabar, da wasu wuraren shakatawa, da na wasanni, a matsayin matakan sassauta dokar da aka kafa don yaki da annobar COVID-19.

Ana bude mallatan kasar ne a wasu kayyadaddun lokuta, kana an haramtawa mata da kananan yara 'yan kasa da shekaru 15 halartar masallatan, har da mutanen dake da barazanar kamuwa da cutar.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China