Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hari kan wani otel a Mogadishu ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 8 yayin da wasu 28 kuma suka jikkata
2020-08-17 09:56:08        cri

Mutane a kalla 8, ciki har da wadanda ake zargin mahara ne, sun mutu, yayin da wasu 28 suka jikkata, sanadiyyar harin da aka kai wani fitaccen otel a birnin Mogadishu na Somaliya a jiya Lahadi.

Kakakin gwamnatin birnin Ismael Mukhtar Omar, ya ce fararen hula hudu da wani darakta a ma'aikatar yada labarai, na daga cikin wadanda suka mutu sanadiyyar harin da wasu 'yan ta'adda suka kai cikin motar dake dauke da bam kan wani babban Otel a birnin Mogadishu.

Ismael Omar ya shaidawa Xinhua ta wayar tarho cewa, an tabbatar da mutuwar mutane 5 ciki har da jami'in gwamnati. Sannan jami'an tsaro sun harbe mahara biyu. Shi ma direban da ya tuka motar dake dauke da bam din ya mutu.

Ya zuwa lokacin hada rahoton, majiyoyi sun bayyana cewa, ana jin amon musayar wuta a cikin otel din.

Babu wanda ya dauki alhakin harin, sai dai kungiyar al-Shabab dake da alaka da kungiyar al-Qaida ta sha kai makamancin harin a baya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China