Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sashen sufurin sama na Afirka ya ji a jika sakamakon tasirin COVID-19
2020-08-17 10:21:39        cri

Wasu alkaluma da kungiyar kasa da kasa mai lura da harkokin sufurin sama ta IATA ta fitar a watan nan na Agusta, sun nuna yadda tattalin arziki, da sashen sufurin sama na nahiyar Afirka, ke shan fama da kalubale, sakamakon mummunan tasirin bullar cutar numfashi ta COVID-19.

Alkaluman sun nuna cewa, akwai yiwuwar wadanda za su rasa ayyukan yi a sashen na sufurin sama a Afirka, ya kai miliyan 3.5. Kafin bullar annobar, guraben ayyukan yi a sashen sun kai miliyan 6.2, wanda hakan ke nuni da cewa, kusan rabin ma'aikatan sashen na iya rasa aikin su a nahiyar.

Alkaluman sun kuma nuna cewa, idan an kwatanta da shekarar 2019, hasashen alkaluman yawan zirga zirgar fasinja ta jiragen sama zai ragu da kaso 54 bisa dari a wannan shekara ta 2020, yayin da kuma ma'aunin GDPn sashen mai yiwuwa zai ragu da kimanin dalar Amurka biliyan 35 ko fiye.

COVID-19 ta gurgunta tattalin arzikin Afirka, ya kuma tsayar da harkokin sufurin sama cik.

A cewar shugaban IATA na yankin Afirka da Gabas ta Tsakiya, hanyar farfado da tattalin arziki da bunkasuwa a Afirka, ita ce sake bude fannonin sufurin jiragen saman nahiyar bisa tsarin kiyaye lafiya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China