Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AfCFTA na sa ran cimma yarjejeniyar cinikayya ta farko a 2021
2020-08-17 11:32:29        cri

Tarayyar Afrika ta sanar da cewa, ana sa ran cimma yarjejeniyar cinikayya ta farko karkashin yankin ciniki cikin 'yanci na nahiyar, a ranar 1 ga watan Junairun 2021, yayin da za a ci gaba da tattaunawa ta kafar intanet.

Sakatare Janar na yankin, Wamkele Mene, ya bayyana cikin watan Afrilu cewa, kaddamar da yarjejeniyar ciniki cikin 'yancin ba zai gudana a ranar 1 ga watan Yuli ba kamar yadda aka tsara, saboda annobar COVID-19.

A cewar AU, yankin zai ba nahiyar damar daidaita sarin samar da kayayyaki, da rage dogaro kan wasu da kuma gaggauta kafa hanyoyin samar da kayayyaki a yankuna, wanda zai bunkasa cinikayya tsakanin kasashen nahiyar.

Wani rahoton bankin duniya ya bayyana cewa, nasarar kaddamar da yankin zai magance tasirin COVID-19 kan ci gaban tattalin arziki ta hanyar bunkasa cinikayya tsakanin yankuna da rage tsadar cinikayyar.

Ya kara da cewa, galibin kudin shigar yankin zai samu ne idan ya fara aiki, kana aka saukaka tsarukan kwastam.

Bugu da kari, rahoton ya ce yankin zai kuma taimaka wajen karawa tattalin arziki karfin jure matsaloli a nan gaba, da maye gurbin yarjejeniyoyin yankuna da inganta tsarukan iyakoki da bada fifiko ga sauye-sauyen da suka shafi cinikayya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China