Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya na amfani da fasahar tattara bayanan barkewar cututtuka don gano yaduwar COVID-19
2020-08-18 09:46:52        cri
Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC, ta ce ma'aikatan cibiyoyin kiwon laifiya a kasar na amfani da wata manhajar musamman dake iya tattara bayanai masu nasaba da barkewar cututtuka, ciki hadda cutar numfashi ta COVID-19 a sassan kasar.

Cikin wata sanarwar da kamfanin dillancin labarai ya samu kwafinta, NCDC ta ce ta hanyar amfani da manhajar SORMAS, ana iya sanya ido kai tsaye kan bayanai daban daban da manhajar ke tattarawa, a kuma yi amfani da su wajan gaggauta daukar matakai.

Wasu gungun masana na Najeriya da na kasar Jamus, da wasu cibiyoyin binciken kimiyya tare da wani kamfanin binciken kiwon lafiya dake Jamus ne suka kirkiri manhajar SORMAS a shekarar 2014, lokacin da cutar Ebola ta barke a yankunan yammacin Afirka, kamar dai yadda cibiyar bincike ta Helmholtz ko (HZI) dake Jamus, daya daga cikin cibiyoyin da suka ba da gudummawa wajen samar da manhajar ta tabbatar.

HZI ta kara da cewa, SORMAS na iya sarrafa bayanai game da barkewar cututtuka, baya ga sanya ido da gano su a kan lokaci kai tsaye ta yanar gizo, a sassan kiwon lafiyar al'umma da suka hada da wuraren jiyyar marasa lafiya, da dakunan gwaje gwaje. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China