Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin ENGO Holding LTD na sa ran bunkasa kasuwancinsa karkashin yarjejeniyar ciniki mara shinge na Afrika
2020-08-18 10:13:36        cri
Bayan shafe watanni 8 da fara samar da kayayyaki a Uganda, kamfanin ENGO Holding LTD na samun tagomashi a fadin nahiyar Afrika.

Sakataren babban daraktan zartaswa na kamfanin, David Beecham Okwere, ya shaidawa Xinhua cewa, bayan sayar da kayayyaki a cikin kasar ta Uganda, kamfanin ya fara fitar da kayayyaki zuwa ketare ta hanyar diloli.

Ya ce kamfanin ya shirya cin gajiyar yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci ta nahiyar Afrika, wadda ke da nufin inganta cinikayya tsakanin kasashen nahiyar da daukaka matsayin cinikayyar Afrika a kasuwar duniya.

Kamfanin ya fitar da kashin farko na wayoyi zuwa Morocco a watan Mayu, inda kasar ta arewacin Afrika ke odar wayoyi 16,000 bayan duk makonni biyu zuwa uku.

Evelyn Anite, ministan kula da zuba jari na kasar, ya shaidawa Xinhua cewa, ba gudunmuwa wajen bunkasa ci gaban tattalin arziki da raya kasar kadai kamfanin yake bayarwa ba, har ma da taimakawa matuka wajen bunkasa kasar ta hanyar yayata ilimi da fasahohin fasahar sadarwa na zamani. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China