Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Luguden wuta ya yi sanadin kisan mayakan BH da dama a arewa maso gabashin Nijerya
2020-08-18 11:32:20        cri
Luguden wuta da rundunar sojin Nijeriya ta yi a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar ya kai ga mutuwar mayakan kungiyar BH da dama.

Kakakin rundunar John Enenche, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, an lalata maboya da cibiyar gudanar da ayyukan kungiyar dake yankunan Tumbuma Baba da Boboshe dake jihar.

Luguden wutan ya biyo bayan sahihan bayanan sirri game da ayyukan mayakan da kuma ayyukan sa ido da aka gudanar, wadanda suka nuna adadi mai yawa na 'yan ta'addan a yankunan, da wajen adana kayayyakinsu da wajen da suke gudanar da taruka,

Kakakin ya ce rundunar za ta ci gaba da kokarinta na kawar da 'yan ta'adda da sauran masu aikata laifuffuka a yankin mai fama da rikici. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China