Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan sufurin Najeriya ya yi na'am da yadda mutane ke shiga aikin gina layin dogo tsakanin Lagos-Ibadan
2020-08-18 21:13:15        cri
Ministan sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa,sama da ma'aikata 20,000 ne suka shiga aikin gina layin dogo mai tsawon kilomita 156 daga Lagos zuwa Ibadan da kamfanin CCECC na kasar Sin yake ginawa.

Ministan ya bayyana haka ne, yayin wani taro aka shirya Abuja, fadar mulkin kasar jiya Litinin. Ya kuma bayyana cewa, yarjejeniyar aikin da aka cimma tsakanin gwamnatin Najeriya da kamfanin CCECC na kasar Sin, tana martaba dokokin wurin.

Ya kara da cewa, yanzu haka, akwai sama da 'yan Najeriya 150 da ake horas a matsayin injiniyoyi a kasar Sin. Haka kuma kasar Sin ta gina cibiyoyin bayar da horo guda biyu a Najeriya, daya a Idu, daya kuma a jami'ar nazarin harkokin sufuri dake garin Daura a jihar Katsina.

Ministan ya ce, galibin kayayyakin aikin da ake amfani da su, a gida Najeriya aka samar da su, abin da ya samar da sabbin guraben ayyukan yi ga mazauna wurin.

Jami'in dake kula da aikin layin dogon Lagos-Ibadan, Yakubu Adogie, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, ana saran fara amfani da layin dogon a wannan shekara. Matakan zai rage tsawon lokacin da ake dauka tsakanin biranen biyu zuwa kasa da sa'o'i biyu, da rage cunkoson ababan hawa da kuma bunkasa tattalin arziki.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China