Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Najeriya: Rancen kudin da kasar Sin take bin Najeriya bai keta ikon mulkin kasar ba
2020-08-20 10:10:23        cri

Jiya Laraba, dan Jarida, kana darektan cibiyar yada labarai tsakanin Afrika da Sin, Ikenna Emuwu, ya wallafa wani bayani a jaridar "The Nation" mai taken "Ikon mulkin Najeriya da rancen kudi da Sin ke bin kasar", a ganin bayanin, Sin ta baiwa kasar rancen kudi bisa ka'idar kasa da kasa, kuma bai keta ikon mulkin kasar ba ko kadan.

Bayanin ya ce, a kwanakin baya wasu 'yan Najeriya sun aza ayar tambaya kan rancen kudin da Sin take bin Najeriya, a ganinsu wasu ayoyi daga cikinsu sun illata ikon mulkin kasar, amma wadannan ayoyi sun yi tanadin cewa, idan Najeriya ba za ta iya biyan kudin cikin lokaci ba, Sin za ta kai kara gaban kotu, kuma a matsayin Nijeriya na kasar dake da ikon mulki, ba za ta iya gudun doka da shari'a ba. Yarjejeniyar rancen kudi ta kasar Sin ya dace da ka'idar kasa da kasa kuma akwai misalai da dama.

Bayanin kuma ya nuna cewa, an fake da batun rancen kudi don tada rikici da nufin dauke hankali daga aikin yaki da cin hanci a kasar. Ya zuwa watan Mayun shekarar bana, yawan basusukan da Najeriya take da su ya kai Naira triliyan 33. Dalilin da ya sa rikicin basusuka ya dabaibaye kasar na da alaka da batun cin hanci da rashawa, wato wadannan rancen kudin da Najeriya ta karba, sun shige aljihunsu wasu, amma kuma kasar ce za ta biya. Abin damuwa shi ne, kasar Najeriya ba ta bayyana yadda take sarrafa basusukan da ta ci a fili ba, amma ba rancen kudi daga kasar Sin ba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China