Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ayarin kwararrun likitocin Sin masu yaki da annoba sun isa Sudan ta kudu
2020-08-20 10:25:26        cri
Tawagar kwararru likitocin da gwamnatin kasar Sin ta tura zuwa Sudan ta kudu domin yaki da annobar COVID-19 sun isa Juba, babban birnin kasar Sudan ta kudu, a ranar 19 ga wata bisa goron gayyatar da gwamnatin Sudan ta kudu ta gabatar, kwararrun za su taimakawa aikin kandagarki da shawo kan annobar a kasar.

Kwararru masanan na kasar Sin wadanda hukumar lafiyar kasar ta kafa, kuma hukumar lafiya ta lardin Anhui ta kasar Sin ta zaba, wadanda suka kushi kwararru 8 daga bangaren kula da cutuka masu yaduwa, da bangaren dakile yaduwar cutuka, da masana hanyoyin numfashi, da kwararru a fannin cuta mai tsanani, da masana kimiyyar gwaje-gwaje, da kwararru a fannin kula da majinyata.

A cewar alkaluman ma'aikatar kula da lafiya ta Sudan ta kudu, ya zuwa ranar 19 ga wata, kasar tana da mutane 2494 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19, daga cikinsu mutane 47 sun mutu. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China