Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta fadada wuraren gwajin ci gaban kirkire-kirkire a fannin hada-hadar ba da hidimomi
2020-08-20 14:48:23        cri

Kwanan baya, majalisar gudanarwar kasar Sin ta tsai da kudurin fadada wuraren gwajin ci gaban kirkire-kirkire a fannin hada-hadar ba da hidimomi daga dukkan fannoni, tare da yarda da wani shiri mai nasaba da hakan a hukumance.

Dangane da lamarin, wani jami'in ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ya ce, kara bude kofar kasar Sin ta fuskar hada-hadar ba da hidimomi ga ketare, sabuwar hanya ce mai muhimmanci da ake bi wajen yin kirkire-kirkire, lamarin da zai kara sabon kuzari ga ci gaban hada-hadar ba da hidimomi na duniya.

Xian Guoyi, shugaban sashen hada-hadar ba da hidimomi na ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ya yi karin bayani da cewa, za a kara yawan wuraren gwaji zuwa 28 a maimakon 17 a baya, ciki hada da biranen Dalian, Xiamen, Qingdao, Shijiazhuang da wasu 5 manyan biranen larduna da dai sauransu, haka kuma za a fadada wasu yankuna. Shirin ya kuma gabatar da ayyukan gwaji 8, da hakikanin matakai 122 daga fannoni 3.

Jami'in ya jaddada cewa, kasar Sin ta kara bude kofar hada-hadar ba da hidimomi ga ketare. "Kasar Sin ta gabatar da matakai 26 a fannonin sufuri, ba da ilmi, kiwon lafiya, hada-hadar kudi, ba da hidimomin musamman da dai sauransu. Alal misali, za a yarda masu ba da hidima na ketare su shiga kasuwar kasar Sin ta hanyoyin biyan kudi a ketaren iyakar kasa, da kuma shigar daidaikun mutane cikin kasar Sin. Kaza lika muddin an bi wasu hanyoyin sufuri wajen jigilar kayayyaki a yankunan Sin ba ta amfani da jiragen ruwa ba, to bisa doka, ba bukatar yin hakan ta kamfanonin kasar Sin kadai. Akwai sauran matakai masu nasaba da harkar ba da izni ga baki, da mazauna lardin Taiwan, ta yadda za su ba da hidimomi a yankunan kasar Sin."

A shekarun baya, tattalin arzikin fasahar zamani ya bunkasa sosai. Bisa tanade-tanaden da ke cikin shirin, kasar Sin za ta kara azama a fannonin ba da hidimomi ta fuskar fasahar zamani da ikon mallakar fasaha, da nazarin magani da sauran sabbin sana'o'i, musamman ma sabunta hanyar sa ido kan bayanai da kuma mu'amalar bayanai. "Za a mai da hankali ga sa ido kan musayar bayanai tsakanin kasashe a sassa daban daban, da yin gwajin tsaron bayanan da ake musaya tsakanin kasashe, da nazari kan yanayin kasuwanci ta fuskar fasahar zamani, da kafa kungiyoyin masana ilmin cinikin fasahar zamani a matakin kasa. Sa'an nan kuma, za a yi gwaji kan kudin Sin RMB da ake amfani da shi kan yanar gizo, da saukaka biyan kudi ta yanar gizo da baki suke yi a kasar Sin, da dai makamantansu, da kuma kara azama kan kirkire-kirkiren ci gaban gasannin kasa da kasa."

A farkon rabin shekarar da muke ciki, yawan cinikin ba da hidimomi ya dan ragu a kasar Sin, amma ana gudanar da cinikin ba tare da wata matsala ba. Yawan cinikin ba da hidimomi da ake fitarwa kasashen ketare ya fi yawan cinikin da ake shigowa da shi daga ketare kyau, musamman ma fannin ba da hidimomin da ke dogoro da ilmi.

Xian Guoyi ya yi nuni da cewa, ko da yake ba a hana yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a wasu sassan duniya ba, lamarin da ya haifar da koma bayan tattalin arzikin duniya, amma an samu kyakkyawan sakamako wajen dalikewa, da kandagarkin yaduwar annobar a kasar Sin, don haka ba a fuskanci illa ga ci gaban cinikin ba da hidimomi a kasar Sin ba. Kaza lika kara yawan wuraren gwajin zai fadada wa kamfanonin cinikin ba da hidimomi kasuwanni, da kara samun zarafi na yin hadin kai da kasashen duniya. "Kara buda kofar kasar Sin, zai taimaka wajen samun babbar kasuwa. Za a kara azama ga fadada bukatu a gida, tare da hada kasuwar gida da kasuwar ketare baki daya, a kokarin kara samar wa masu ba da hidimomi a gida da wajen kasar Sin kasuwanni. Sa'an nan kasar Sin za ta raya cinikin fasahar zamani, da cinikin ikon mallakar fasaha, da ba da ilmi ta yanar gizo da sauran sabbin hidimomi, ta yadda za su kara kuzari ga ayyukan sayar da kayayyaki a ketare. Za kuma a kara shigar da hidimomin da suka shafi ayyukan kera kaya, cikin tsarin kasa da kasa na samar da kaya, tare da sa kaimi ga zuba albarkatu cikin sabbin sana'o'i. Har ila yau, za a fadada wuraren gwaji da kara samar wa kasar Sin, da kasashen da suke aiwatar da shawarar 'ziri daya da hanya daya' fannonin yin hadin gwiwa, ta fuskar cinikin ba da hidimomi. Ma iya cewa, fadada wuraren gwaji, zai kara ingiza ci gaban cinikin ba da hidimomi na kasar Sin yadda ya kamata, kana kuma zai kara kuzari ga ci gaban cinikin ba da hidimomi a duniya. " (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China