Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar MNJTF ta mikawa Najeriya mutane 94 da ta ceto daga mayakan Boko Haram
2020-08-20 20:48:21        cri
Dakarun hadin gwiwar kasashen kamaru da Chadi da Nijar da Najeriya dake yaki da mayakan Boko Haram a yankin tafkin Chadi (MNJTF), sun mikawa jihar Borno dake tarayyar Najeriya, mutane 94 da mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da su a yankin tafkin Chadi.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Borno Isa Gusau ya fitar, ta bayyana cewa, rundunar hadin gwiwar ta yi nasarar ceto mutanen, da suka hada da maza baligai 37 da mata baligai 17 da yara 40 ne, yayin wani musayar wuta da suka fafata da mayakan a yankin na tafkin Chadi.

Kwamishinan shari'a na jihar Borno, Kakashehu Lawal, wanda ya karbi mutanen da aka ceto, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, gwamanti za ta gudanar da bincike, da sake musu tunani, ta kuma hade wadanda ake ceton da iyalansu, ta yadda za su yi rayuwa kamar kowa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China