Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban AU ya yi alkawarin goyon baya AfCFTA
2020-08-21 09:38:45        cri
A matsayinsa na shugaban AU, shugaban Afrika ta kudu, Cyril Ramaphosa ya yi alkawarin nuna cikakken goyon baya ga aiwatar da yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci ta nahiyar Afrika.

Wata sanarwar da Tyrone Seale, mukaddashin kakakinsa ya fitar, ta ce Cyril Ramaphosa ya bayyana goyon bayan nasa ne ga Sakatare Janar mai kula da harkokin yankin wato Wamkele Mene, yayin bikin mika sakatariyar yankin a farkon wannan mako a birnin Accran Ghana.

Kasashe mambobin AU ne suka zabi Ghana a matsayin mazaunin Sakatariyar, yayin taro na 12 da kungiyar ta gudanar cikin watan Yulin bara a birnin Niamey na Niger.

Sanarwar ta ce a madadin AU da nahiyar Afrika, Cyril Ramaphosa ya bayyana godiya ga gwamnati da al'ummar Ghana dangane da samar da mazauni ga sakatariyar.

Cyril Ramaphosa, ya kuma tabbatar da kudurin AU na cimma nasarar aiwatar da yarjejeniyar, a matsayin ingantacciyar hanyar bada gudunmmawa ga raya tattalin arzikin Afrika tare da yin maraba da ci gaban da aka samu zuwa yanzu, dangane da aiwatar da batutuwan da aka cimma yayin taron AU na 12. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China