Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CNSP: Mali za ta bude kan iyakokinta da sararin sama bayan juyin mulki
2020-08-21 10:45:54        cri
Kwamitin fafutukar ceto al'ummar kasa CNSP, kwamiti ne na rikon kwarya wanda sojojin da suka yi bore a kasar Mali suka kafa, sun sanar a daren Alhamis cewa za a bude kan iyakokin kasar Mali da sararin samaniyar kasar a yau Juma'a.

A wani takaitaccen jawabi da aka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun mataimakin kwamitin CNSP, Kanal Malick Diaw, ya sanar cewa za a sake bude kan iyakokin kasar Mali na kasa da na sama da tsakar daren Juma'a.

Sabuwar hukumar sojojin dake jagorancin Mali ta ce, an dauki dukkan matakan tsaron da suka dace domin tabbatar da zirga-zirgar jama'a da kayayyakinsu a kasar.

Sa'o'i kadan bayan tursasawa shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita yin murabus a ranar Talata, kwamitin CNSP ya fitar da sanawarta ta farko. Inda Colonel-Major Ismael Wague, kakakin CNSP, ya sanar da jerin matakan da aka dauka, da suka hada da rufe dukkannin iyakokin kasar ta sama da ta kasa har sai abin da hali ya yi, da kafa dokar takaita zirga-zirga a kasar daga karfe 9 na dare zuwa 5 na safe.

Sai dai kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS, ta yi kakkausar suka game da hambarar da gwamnatin shugaba Keita wacce aka zaba bisa tsarin demokaradiyya. Da yammacin ranar Talatar ECOWAS ta yanke shawarar rufe dukkan iyakokin kasar da kuma yanke duk wata alaka da huldar cinikayya da mu'amalar tattalin arziki dake tsakanin kasashen mambobin ECOWAS da Mali, har zuwa lokacin da kasar Mali ta maido da amfani da kundin tsarin mulkinta. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China