Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ta bukaci kwamitin sulhu na MDD da ya farfado da takunkumin da ya taba kakaba wa Iran
2020-08-21 21:41:27        cri
Kasar Amurka ta aika wasika ga kwamitin sulhu na MDD, inda ya bukaci kwamitin da ya dawo da takunkumin da ya taba kakaba wa kasar Iran.

Dangane da wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yau cewa, kasar Amurka ta riga ta janye daga yarjejeniyar batun nukiliyar kasar Iran, don haka yanzu, ba ta da ikon sa kaimi da a gaggauta farfado da takunkumin da aka kakaba wa kasar Iran.

A ranar 20 ga wata, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya aikawa shugaban kwamitin sulhu na MDD wasika, inda ya bukaci a gaggauta farfado da takunkumin da aka kakabawa kasar Iran, bisa kuduri mai lamba 2231 na kwamitin sulhu na MDD, kuma, ya ce, ya kamata a kammala wannan aiki cikin kwanaki 30.

Da yake tsokaci kan wannan harka, Zhao Lijian ya ce, kasashen Sin, Rasha, Burtaniya, Faransa, Jamus da Iran sun riga sun gabatar da wasikunsu ga shugaban kwamitin sulhu na MDD, kuma, ministocin harkokin wajen kasashen Burtaniya, Faransa da Jamus sun fidda sanarwa, inda suka nuna kin amincewarsu kan mataki na kasar Amurka. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China