Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: An samu rahoton bullar Ebola 100 a yammacin Kongo Kinshasa
2020-08-22 16:16:56        cri
An samu rahoton bullar cutar Ebola kimanin 100 a lardin Equateur dake yammacin jamhuriyar demokaradiyyar Kongo, hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma'a a Kinshasa.

A cewar sanarwar, cutar ta bulla a wannan karo na 11 tun daga ranar 1 ga watan Yuni a birnin Mbandaka, babban birnin lardin Equateur, inda ta riga ta bazu zuwa shiyyoyi 11 daga cikin shiyyoyin kula da lafiya 17 dake wannan lardi.

Daga cikin jimillar rahotanni bazuwar cutar guda 100, an tabbatar da 96, yayin da guda hudu har yanzu ba a tabbatar da su ba. Baki daya mutane 43 ne suka mutu a sanadiyyar barkewar annobar a wannan bangare na kasar, kamar yadda bayanan da kwamitin dakile cutar na hukumar lafiyar kasar ke fitarwa duk mako ya nuna.

Hukumomin lafiyar kasar sun ayyana barkewar cutar a karo na 11 ne kwanaki kadan bayan shawo kan annobar da ta barke a karo na 10 a yankin kula da lafiya na Beni, dake arewacin lardin Kivu a gabashin kasar wanda yayi sanadiyyar kashe sama da mutane 2,000.

A shekarar 2018, a wannan lardi na Equateur ne aka samu barkewar Ebola a karo na tara inda aka samu nasarar dakile ta cikin kasa da watanni uku, mutane 54 ne suka kamu, sai kuma mutane 33 da cutar ta hallaka.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China