Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya jaddada muhimmancin inganta cigaban yankin kogin Yangtze
2020-08-22 17:01:41        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada muhimmancin cigaba da lalibo ingantattun hanyoyin bunkasa dunkulewar yankin kogin Yangtze, ta hanyar mayar da hankali kan muhimman ayyukan samar da cigaba.

Xi, ya yi wannan tsokaci ne a yayin taron tattaunawa da aka gudanar a ranar Alhamis a Hefei, babban birnin lardin Anhui dake shiyyar gabashin kasar Sin.

Cikin jawabin da ya gabatar a lokacin taron, shugaba Xi ya ce, tsarin dunkulewar shiyyar da hadewar bangarorin kayayyakin more rayuwar jama'a sun taka muhimmiyar rawa a aikin kandagarki da yaki da annobar COVID-19 gami da farfadowar tattalin arziki.

Ya bukaci a samu fahimta mai zurfi game da matsayin yankin kogin da irin alfanun da yake da shi ga cigaban tattalin arzikin kasar Sin da zamantakewar alumma, domin a samu damar kara inganta dunkulewar bunkasuwar shiyyar a daidai lokacin da ake fama da yanayi na rashin tabbas.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China