Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda kauyen Xinzha ya kawar da talauci ta hanyar sarrafa kayan kamshi
2020-08-22 20:32:47        cri

Kauyen Xinzha wani karamin kauye ne dake yankin Xizang mai cin gashin kansa na kasar Sin, kauyen na da bunkasuwar harkokin zirga-zirga da albarkatu iri-iri.

Magatakardan reshen JKS na kauyan Xinzha, kana shugaban ma'aikatar sarrafa kayan kamshi da magungunan gargajiya, Labaciren, ya bayyana cewa, mutanen kauyen sun kaura zuwa nan domin bala'u da karancin ruwa da suke fama da su a tsohon garinsu, yanzu, akwai iyalai kimanin 39 dake kunshe da mutane 127 da suke zama a wannan kauye. Kafin su kaura zuwa nan, yawancin lokuta suna samun kudin shiga ta hanyar hakar maganin gargajiya da ayyukan gona, babu wanda ya fita waje domin neman aikin yi.

Sabo da garin Laduo shi ne asalin reshen kudu na likitancin Zang, kuma kauyen Xinzha yana da albarkatun maganin gargajiyar Zang, shi ya sa, magatakardan reshen JKS na kauyan Xinzha Labaciren ya yi tunanin cewa, ya dace a kafa ma'aikatar sarrafa kayan kamshi da magungunan gargajiya a wannan wuri.

Bayan da aka bude wannan ma'aikata, masu fama da talauci a kauyen, da nakasassu da sauran mutanen kauyen suna iya yin ayyuka a ma'aikatar, ta yadda, suke samun kudin shiga. Kana, a kowace shekara, kowane mutum yana iya samun kudin shiga na yuan dubu goma da dari hudu. Ban da haka kuma, a karshen kowace shekara, suna iya samun karin riba da ma'aikatar ta samar musu.

Bugu da kari, ma'aikatar tana sayen magungunan gargajiyar Zang da mutanen kauyen suka shuka, ta yadda mutanen kauyen suke samun karin kudaden shiga. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China