Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An fara gina cibiyar cinikin hakkin mawallafi ta CMG a birnin Shanghai
2020-08-22 21:39:28        cri

Yau Asabar, an fara gina cibiyar cinikin hakkin mawallafi ta babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a birnin Shanghai, kuma ana shirin kafa cibiyar nazarin raya birane a sabon zamani. Mataimakin ministan fadakar da jama'a, kana shugaban CMG Shen Haixiong da mataimakin darektan kwamitin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na birnin Shanghai Gong Zheng sun halarci bikin kaddamar da aiki, inda suka gabatar da jawabi.

An ce, cibiyar da za a gina zata kafa manyan tsare-tsare guda uku da suka hada da tsarin tafiyar da na'urori, da tsarin kula da hakkin mawallafi, da kuma tsarin gudanar da ayyuka, bisa hakkin mawallafi masu inganci da fasahohin yada labarai na 5G+4K/8K+AI wanda CMG yake da su, domin habaka ayyukan amfanin hakkin mawallafi yadda ya kamata. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China