Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta harba sabon tauraron dan adam da ake iya sarrafa shi da na'ura
2020-08-23 17:08:24        cri

Kasar Sin ta yi nasarar harba sabon tauraron dan adam mai daukar hotuna da ake iya sarrafata da na'ura wanda aka harba da misalin karfe 10:27 na safiya, agogin Beijing, a cibiyar harba tauraron dan adam na Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar.

Tauraron, samfurin Gaofen-905, an harbe shi zuwa tsakiyar sararin samaniya ta hanyar amfani da na'urar harba roka samfurin Long March-2D.

Gaofen-905 yana da karfin daukar bayanai. Za a yi amfani da shi ne wajen aikin safiyo, da tsara birane, da tabbatar da hakikanin yanayin filaye, da aikin tsara hanyoyin mota, da kiyasin samun yabanyar amfanin gona, da kuma yin kandagarkin bala'o'i.

Tauraron zai kuma taimaka wajen samar da bayanai ga gudanarwar shawarar ziri daya da hanya daya.

An kuma harba wasu taurarin dan adam din masu ayyuka daban daban da ake kira da suna Tiantuo-5 ta hanyar rokar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China