Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wayar salula ta kasance kayan aikin gona a yankin Jalaid
2020-08-23 20:19:19        cri

Yankin Jalaid yana kudancin gandun dajin Greater Khingan dake jihar Mongolia ta gida ta kasar Sin, inda ake mallakar gonakin shuka shinkafa masu inganci.

A watan Satumban shekarar 2017, an fara gina sansanin aikin gona na zamani mai fadin hekta dubu 40 a yankin Jalaid bisa amincewar gwamnatin kasar Sin, inda aka shuka shinkafa a gonakin sansanin masu fadin hekta dubu 30.

Mataimakin sakataren kwamitin JKS na garin Haolibao Lu Yongze ya bayyana cewa, "Mun gyara tsarin yin shuke-shuke ta hanyar shuka shinkafa ba tare da amfani da sinadaran zamani ba, domin kara kudin shigar manoman garinmu."

Garin Haolibao yana da gonaki masu fadin hekta 18667, inda ake shuka shinkafa tare da kiwon kaguwa da karamin lobster da kifi da agwagwa a gonakin ruwa, saboda ba su yin amfani da sinadaran zamani, hakan ba ma kawai ya kara shinkafar da ake girba ba ne, har ma ya sa ana kashe kwari masu lahanta shuke-shuke ba tare da gurbata muhalli ba.

A sansanin gonakin zamani, an fitar da shirin yin hayar gona mai fadin hekta 0.067 mai taken "ina da gona a Jalaid", wanda ya yi hayar gonar a nan yana iya duba yadda shinkafa ke girma ta hanyar manhajar wayar salula, bayan an girbe shinkafa a lokacin kaka, masu aikin dake sansanin za su aika shinkafa da karamin lobster da kaguwa da agwagwa zuwa ga gidan mai yin hayar gonar sau daya a kowanen watanni uku ko shekara daya.

Don haka wayar walula ta kasance kayan aikin gona, duk da cewa masu yin hayar gonakin suna da nesa da gonar, amma suna iya cimma burinsu na shuka shinkafa a gonaki ta hanyar yin amfani da manhajar wayar salula.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China