Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Abubuwan fashewa sun hallaka jami'an tsaro 4 a tsakiyar Mali
2020-08-24 10:06:36        cri
Jami'an tsaro 4 daga rundunar wanzar da zaman lafiya aka hallaka, sannan wani mutum guda ya samu mummunan rauni a ranar Asabar a lokacin da motar da suke ciki ta haura ta kan wasu abubuwan fashewa a yankin Mopti dake shiyyar tsakiyar Mali, hukumar tsaron kasar Mali ce ta tabbatar da faruwar lamarin.

Babban jami'in hukumar tsaro na shiyyar Bandiagara, ya ce, motar jami'an tsaron ta taka abubuwan fashewa a yankin, sai dai bai yi cikakken bayani game da lamarin ba.

Babu wani mutum ko wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin yayin da ake tsaka da fuskantar dambarwar siyasa a kasar ta Mali.

Ko da a yammacin ranar Alhamis, a yankin Gao dake arewacin Mali, wasu 'yan bindiga da ba a tantance ko su wane ne ba suka bude wuta kan wasu taron matasa, inda suka kashe mutane uku da kuma jikkata mutum guda, wasu da suka shaida faruwar lamarin sun fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

A cewar tawagar shirin wanzar da zaman lafiya ta MDD dake Mali MINUSMA, lamarin ya shafi batun ramuwar gayya ne a tsakanin al'ummun kasar.

Wadannan hare-haren na zuwa ne bayan da sojojin kasar masu bore suka hambarar da gwamnatin kasar Mali a ranar 18 ga wannan wata. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China