Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masani: Karfafa dangantakar Sin da Afrika muhimmin jigo ne na farfadowar tattalin arziki bayan fama da annobar COVID-19
2020-08-24 10:35:35        cri
Peter Kagwanja, shugaban cibiyar nazarin al'amurran Afrika, wani kwararren masani daga shiyyar, ya bayyana cikin wani sharhi da aka wallafa a jaridar Sunday Nation cewa, yayin da duniya ke ci gaba da fama da matsalolin annobar COVID-19, bunkasa ayyukan masana'antu da fasahar kirkire-kirkire muhimman hanyoyi ne ga shirin fardadowar Afrika daga tasirin annobar COVID-19.

Kagwanja ya rubuta cikin sharhi cewa, yayin da ake kara samun hallayyar nuna wariya, da kariyar ciniki, da kuma janyewar zuba jari daga abokan huldar kasuwancin Afrika na yammacin duniya, yin hadin gwiwa da kasar Sin zai samar da muhimman damammaki game da dabarun kasashen Afrika na farfadowa daga illolin annobar COVID-19, yayin da bunkasa masana'antu zai taimaka wajen kawar da talauci, da samar da guraben ayyukan yi gami da abubuwan dogaro da kai.

Ya ce, matakin yawaitar nuna wariyar tattalin arziki na wasu kasashe, da kariyar ciniki, da nuna son kai na yammacin duniya, ya kara daga matsayin muhimmancin dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika da bukatar gaggauta zurfafa hadin gwiwa a tsakaninsu.

Kagwanja ya ce, tun daga watan Fabrairu, kasar Sin ta yi hadin gwiwa tare da kasashen Afrika 54 domin yaki da annobar COVID-19.

A cewar masanin, tallafin raya cigaba da kasar Sin ke samarwa ya bada gagarumar gudunmawa ga Afrika, wajen shirin yaki da fatara a nahiyar.

Kasar ta nahiyar Asiya ta yi amfani da huldar diflomasiyyarta da zuba jari wajen tallafawa ajandar samar da dauwwamammen ci gaban nahiyar Afrika nan da shekarar 2063. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China