Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sabon gidan Bai Malazhen da yadda take jin rayuwa
2020-08-24 13:09:44        cri

A kauyen Zhaza na garin Zhegu na gundunar Cuomei dake birnin Shan'nan na yankin Tibet mai cin gashin kansa, akwai magidanta 169 da suka ci gajiyar sabbin gidajen shirin kawar da kangin talauci. Bai Malazhen mai iyalai 7 na daya daga cikin su

A halin yanzu dai, Bai Malazhan mai shekaru 44 a duniya tana zama ne a wani sabon gida mai hawa biyu, salon irin na kabilar Tibet.

A baya, mazauna kauyen Zhaza suna zama a kan tsauni, an gina gidaje a duk inda yake so, sakamakon haka, ba su da tsari, ga kuma cunkuso, kuma babu hanyoyi masu kyau. Bai Malazhen ta ce, gidanta ba shi da kyau, dakuna 3 ne kawai, dukkan iyalansu 7 sun kwana a cikin daki 1.

A shekarar 2018, an fara aiwatar da shirin kaurar da kauyawa zuwa sabbin gidaje, inda kwamitin gudanarwa na kauye ya yiwa kauyawa bayani kan wannan shiri. Bai Malazhen ta yi farin ciki sosai da sanin labari. Bisa shirin da aka tsara, kauyawa sun biya kudi kalilan don gina sabbin gidaje.

Tun lokacin da ta shiga sabon gidanta mai fadin haske, Bai Malazhen tana murna a zuciyarta, tana fara'a idan tana magana. Mene ne rayuwa mai dadi? Watakila amsar tana cikin murmushin farin ciki da ake yi har zuciya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China