2020-08-24 14:08:08 cri |
Mr. Wang wanda ya bayyana haka kwanakin baya, yayin zantawa da takwaransa na kasar Morocco Nasser Bourita ta wayar tarho, ya ce, hadin gwiwar kasashen bisa manyan tsare-tsare karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping na kasar Sin da Sarki Mohammed VI na Morocco, ta jure tasirin annobar COVID-19, har ta kara bunkasa.
Ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa kokarin kasar Morocco na yaki da annobar CIVID-19, tare da dawo da harkokin tattalin arziki, da rawar da kasar ke takawa a harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya.
Wang ya yi nuni da cewa, da zarar kasar Sin ta yi nasarar samar da riga kafin COVID-19, har aka fara amfani da ita, duniya da kasashen Afirka na daga cikin wadanda za su fara amfana.
A nasa bangare Bourita, ya bayyana cewa, kwarewar da kasar Sin ta samu a fannin yaki da COVID-19, ta taimakawa kasarsa, kuma Moroccon na da tabbaci kan fasahar kasar Sin a fannin samar da riga kafi. A don haka, Morocco tana fatan nan ba da dadewa ba, sassan biyu za su sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa a tsakaninsu. (Ibrahim)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China