Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'an tsaron tekun Libya sun gano gawar 'yan ci rani 22 a yammacin tekun kasar
2020-08-24 16:34:45        cri
Hukumar kula da bakin haure ta kasa da kasa IOM, ta sanar cewa, dakarun tsaron tekun Libya sun tsinto gawar bakin haure kimanin 22 daga gabar tekun birnin Zwara.

Federico Soda, jami'in hukumar ta IOM ya wallafa a shafin Twita cewa, an samu wannan mutuwar mai tayar da hankali ne sakamakon tsananin tashin hankali da matsanancin talauci dake tilastawa mutanen yunkurin tsallaka zuwa kasashen ketare, da kuma gaza daukar matakan dakile yawaitar kwararar bakin hauren.

Libya ta zama wata matattarar bakin haure inda dubban 'yan ci rani ke neman tsallakawa zuwa kasashen Turai ta hanyar tekun Mediterranea, tun bayan kifar da gwamnatin marigayi shugaban kasar Libya Muammar Gaddafi wanda aka kashe a shekarar 2011, lamarin da ya haifar da tabarbarewar tsaro da tashe tashen hankula a kasar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China