Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manufar hana sun kifi a kogin Yangtze
2020-08-24 16:42:12        cri

A yayin wani rangadin da ya yi a birnin Hefei, fadar mulkin lardin Anhui dake gabashin kasar Sin, Xi Jinping, shugaban kasar, ya nanata muhimmancin manufar hana sun kifi cikin shekaru 10 masu zuwa a kogin Yangtze na kasar, inda ya ce an dauki manufar ne domin tabbatar da moriyar daukacin al'ummar kasar, da samun wani muhalli mai kyau a nan gaba.

 Ban da wannan kuma, shugaban na kasar Sin ya ce, ya kamata a ba da tallafi ga masunta, ta yadda za su yarda su daina kamun kifin, gami da samun damar kyautata zaman rayuwarsu.

Wannan kulawar da shugaban ya bai wa masunta, ta sa suka yarda da dakatar da aikinsu na kamun kifi a kogin Yantze, kogi mafi tsawo a nan kasar Sin, kuma mafi tsawo na uku a duk duniya, gami da fara gudanar da sauran sana'o'i, misali kiwon kifi, da bude wurin cin abinci, da dai sauransu, tare da samun zaman rayuwa mai inganci. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China