Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin wayar salula na Vivo ya kulla alaka da Jumia don kara sayar da hajojinsa a Kenya
2020-08-25 09:55:40        cri
Jiya Litinin ne, kamfanin kasar Sin mai samar da wayoyin salula na Vivo, ya sanar da kulla hadin gwiwa da kamfanin cinikayya ta yanar gizo a Afirka wato Jumia, da nufin fadada tasirinsa a kasuwar kasar Kenya.

Shugaban kamfanin Vivo a kasar Kenya Arthur Xian, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, yin hadin gwiwa da Jumia, zai bunkasa kokarinsu na samarwa masu sayayya wayoyin salula iri-iri masu inganci da kuma araha.

Xian ya ce, kamfanin na fatan kara samar da wayoyin salula na zamani masu inganci ta kasuwar Jumia, a wani mataki na biyan bukatun karuwar masu sayayya na kasar Kenya.

Ya bayyana cewa, hadin gwiwar, za ta kara shigar da wayoyin salula na zamani cikin kasar, da fadada burin kasuwar Jumia na shigar da fasahar zamani a cikin nahiyar Afirka. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China