Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararrun likitocin Sin sun koyar da jami'an lafiyar Sudan ta kudu kan yaki da COVID-19
2020-08-25 10:10:35        cri

Tawagar kwararrun likitocin da gwamnatin Sin ta tura zuwa kasar Sudan ta kudu a ranar Litinin sun fara aikin horas da ma'aikatan lafiyar kasar ta gabashin Afrika game da yaki da annobar COVID-19.

Jagoran tawagar, Liang Chaozhao ya ce, shirin bada horon na kwanaki uku zai taimakawa kasar Sudan ta kudu game da yaki da annobar COVID-19 kuma zai baiwa kwararrun lafiya na kasashen biyu damar yin musayar kwarewa a tsakaninsu.

Liang ya ce, yana da muhimmanci ga ma'aikatan lafiya su fahimci yadda za su kare kansu, domin su samu damar yaki da cutar yadda ya kamata. Don haka, horon zai taimaka musu wajen yaki da annobar ta COVID-19.

Horon ya samu halartar ma'aikatan lafiya na Sudan ta kudu sama da 70, inda aka horar da su kan yadda za su kare kansu da kuma tinkarar yaki da annobar COVID-19.

Daya daga cikin mahalarta shirin bada horon, Elizabeth Achan ya ce, horon yana da kyau, kuma a bayyane yake. Ya ce ya koyi yadda zai kare kansa a lokacin da yake bakin aikin yaki da cutar COVID-19. Har ma ya bukaci a tsawaita wa'adin bada horon domin wasu karin ma'aikatan lafiyar kasar su amfana. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China