Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Sabon tsarin neman ci gaba yana shafar musayar dake tsakanin kasa da kasa
2020-08-25 10:43:46        cri
Jiya Litinin, babban sakataren kwamitin tsakiyar Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, shugaban kasa, kana, shugaban rundunar sojojin kasar Sin, Xi Jinping ya jagoranci taron karawa juna sani na masana a fannin tattalin arziki da zaman al'umma, inda ya jaddada cewa, daga shekarar 2021 zuwa shekarar 2025, kasar Sin za ta shiga sabon matakin neman bunkasuwa, a don haka, ya kamata mu yi hangen nesa, da yin nazari kan sabbin harkoki, domin tsara sabon shirin neman ci gaba yadda ya kamata.

Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin tana neman dauwamammen ci gaba mai inganci cikin sauri, da martaba ka'idar adalci da tsaro. Ya kamata a inganta musayar dake tsakanin bangarori daban daban na kasar Sin, da musayar dake tsakanin kasar Sin da kasashen ketare, domin ya dace da halin da muke ciki. Sabon tsarin neman ci gaba yana nufin bude kofa da kuma yin musaya a tsakanin kasa da kasa.

Xi Jinping ya ce, ya kamata mu samar da sabbin damammakin ci gaba ta hanyar yin kirkire-kirkire bisa kimiyya da fasaha, da tsayawa tsayin daka wajen yin kirkire-kirkire bisa ka'idar bude kofa ga waje. Haka kuma, ya dace a karfafa musayar kimiyya da fasaha tsakanin kasa da kasa.

Shugaba Xi, ya jaddada cewa, ya kamata mu kara karfinmu da daukar matakan kawar da tsohon tsarin dake hana bunkasuwarmu, da kyautata tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin, domin inganta tsarin tafiyar da harkokin kasa, ta yadda zai dace da halin da muke ciki a sabon zamani. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China