Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Birnin Chongqing ya dauki matakai da dama na inganta muhallin halittu
2020-08-25 17:07:44        cri

Yankin kiyaye muhallin halittu na Jinyunshan ya kasance tamkar "huhu" ga birnin Chongqing, ma'ana wato yana taka muhimmiyar rawa ga ingancin iska da ma muhalli na wurin. Duk da haka, a baya an taba fuskantar matsalolin lalacewar yanayin wurin, a sakamakon yadda aka yi ta gine-gine da bunkasa yawon shakatawa ba bisa ka'ida ba a wurin.

Domin daidaita matsalar, a watan Yunin shekarar 2018, an kaddamar da aikin gyaran yankin. Bisa matakan da aka dauka cikin shekaru biyu da suka wuce, kawo yanzu, an rufe masaukan baki sama da 150 da suka gudana ba bisa ka'ida ba, tare da dasa bishiyoyi kusan dubu 660, matakin da ya sa yankin ya samu gyaran fuska sosai. Baya ga inganta muhallin wurin, an kuma kara kyautata rayuwar mazauna wurin. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China