Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na aiki tukuru wajen aiwatar da shawarar G20 game da yafe basussuka
2020-08-25 21:06:33        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian ya ce, Sin na aiki tukuru wajen aiwatar da shawarar kungiyar G20 game da yafe basussuka.

Zhao Lijian wanda ya yi karin haske game da hakan, ya ce a yanzu haka, Sin ta karbi takardun neman yafe bashi daga kasashe sama da 20. Kaza lika ya zuwa karshen watan Yuli, Sin ta cimma matsaya tare da kasashe sama da 10, game da batun na yafe bashi, tana kuma karfafa tattaunawa da tsare tsare, da kasashen da suka mika mata bukatun su, inda kuma ake ci gaba da aiki kan bukatun.

Zhao Lijian ya ce, Sin na dora muhimmancin gaske, game da tasirin da cutar COVID-19 ta yi a Afirka, da ma sauran kasashe masu tasowa, ta kuma fahimci matsin da kasashen ke fuskanta game da biyan bashi. Kari kan hakan, Sin na taimakawa shirin kasa da kasa, wajen aiwatar da manufofin hadin gwiwa don rage nauyin bashin da ake bin kasashe, tare da samar da karin kayayyakin aiki na shawo kan wannan annoba, da kuma daidaita yanayin tattalin arzikin kasashen. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China