Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yankin musamman na Shenzhen ya cika shekaru 40 da kafuwa
2020-08-25 21:12:34        cri

Ranar 26 ga watan Agustar bana, yankin musamman na tattalin arziki na Shenzhen dake lardin Guangdong na kasar Sin, ke cika shekaru 40 da kafuwa, A cikin wadannan shekaru 40, birnin Shenzhen ya sauya daga wani karamin kauyen kamun kifi, zuwa babban birnin zamani, inda mazauna sama da miliyan 10 ke rayuwa, wanda hakan ya shaida manyan sauye-sauyen da aka samu a kasar Sin, tun bayan da aka fara aiwatar da manufar kwaskwarima.

Bisa matsayinsa na yankin musamman na tattalin arziki na farko a kasar Sin, Shenzhen ya samu ci gaba cikin sauri, karkashin jagorancin shugabanni da dama.

A ranar 8 watan Disamban shekarar 2012, babban sakataren JKS Xi Jinping, ya je dutsen Lotus, domin mika fure ga mutum mutumin marigayi Deng Xiaoping, daga baya ya dasa wani itace a wurin, hakika a lambun shan iska na tsirrai na tafkin Xianhu na birnin Shenzhen dake kusa da dutsen Lotus, akwai wani itace daban, wanda marigayi Deng Xiaoping ya dasa a shekarar 1992, yayin da yake rangadin aiki a nan, wanda ya bude wani sabon shafi na yin gyare-gayre a kasar Sin.

Bayan da babban sakatare Xi ya tashi daga Shenzhen, sai ya sauka biranen Zhuhai da Foshan da Guangzhou, inda sau da dama ya jaddada cewa, yin gyare-gyare da bude kofa ga ketare, suna da babbar ma'ana ga makomar kasar Sin.

A watan Oktoban shekarar 2018, lokacin da aka cika shekaru 40 da fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga ketare a kasar Sin, babban sakataren Xi ya sake zuwa Shenzhen, inda ya sake sanar da cewa, kasar Sin ba za ta daina yin kwaskwarima ba, haka kuma ba za ta daina bude kofa ga ketare ba.

A karkashin jagorancin Xi, kasar Sin ta samu babban sakamako a fannoni daban daban. Alal misali gina babban yankin lardin Guangdong da Hong Kong da Macau, da gina yankin cinikiyya maras shinge na Hainan, da aiwatar da manufar rage shinge ga 'yan kasuwan ketare, da kara habaka zumuntar dake tsakaninta da sauran kasashen duniya bisa shawarar ziri daya da hanya daya.

Abun farin ciki shi ne, duk da cewa ana yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19 a yanzu, duk da haka kasar Sin ba ta daina kokarinta na yin gyare-gyare ba, inda har ta dauki sabbin matakai a jere, domin kara kyautata ayyukan da take gudanarwa.

Kamar yadda shugaba Xi ya taba bayyanawa, idan ana son gina kasar zamani mai karfi na gurguzu, to dole sai an rika yin kokari. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China