Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
NCWS ta yi kira da a kara azama wajen dakile COVID-19
2020-08-26 09:36:20        cri
Majalisar kungiyoyin mata ta Najeriya (NCWS) ta yi kira da a kara zage damtse a kokarin da ake yi na rage yawan wadanda ke kamuwa da cutar numfashi ta COVID-19, a yayin da kasar ta ke fama da kwayar cutar.

Shugabar gamayyar ta NCWS Laraba Shoda, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, yanayin da ake ciki a Najeriya a halin yanzu abin damuwa ne, duba da yadda ake samun Karin mutane dake harbuwa da wannan cuta a cikin kasar.

Ta ce, idan har gwamnatocin jihohi da na tarayyar kasar suka martaba dokokin kare kai daga kamuwa da wannan cuta, hakan zai taimaka matuka wajen rage yaduwarta da ma gano wadanda tuni suka harbu da cutar.

A cewarta, a yayin da ake bin wadannan ka'idoji sau da kafa, ya zama wajibi jama'a su rika kula da matakan tsafta, kamar yawaita wanke hannaye yadda ya kamata, da kuma barin tazara a tsakanin juna.

Shoda ta bayyana cewa, annobar ta yi wa tattalin arzikin kasar kamun kazar kuku, don haka, ya zama wajibi a hada karfi da karfe don farfado da tattalin arzikin. Tana kuma yi kira ga gwamnati, da ta rage farashin kyallen rufe baki da hanci da sinadarin wanke hannu, ta yadda kowa ne dan Najeriya zai iya saya ba tare da wata matsala ba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China