Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO:Afirka ta yi ban kwana da cutar shan-Inna
2020-08-26 09:53:10        cri
Hukumar shiyyar Afirka dake ba da shaidar rabuwa da cutar shan-Inna ko Polio (ARCC) ta sanar jiya Talata a hukunce cewa, shiyyar ta Afirka ta rabu da kwayar cutar ta Polio.

Hakan na nuna cewa, an kawar da kwayar cuta ta biyu daga nahiyar, bayan da aka ga bayan cutar kyanda shekaru 40 da suka gabata.

A shekarar 1996 ne dai, shugabannin Afirka suka yanke shawarar kawar da cutar shan-Inna a fadin nahiyar, yayin babban taron kungiyar hadin kan Afirka na 32 da ya gudana a kasar Kamaru. A wancan lokaci, an yi hasashen cutar tana nakasa yaran da yawansu ya kai 75,000 a ko wace shekara a nahiyar.

Tun a shekarar 2016 dai, ba a samu ko da yaro daya da ya kamu da kwayar cutar ba a Najeriya. A cewar WHO, matakan kawar da cutar, sun taimaka wajen hana yara miliyan 1.8 kamuwa da cutar dake shanye kafafu har abada, baya ga rayuka a kalla 180,000 da aka yi nasarar kubutarwa daga kamuwa da wannan cuta.

Darektan hukumar WHO mai kula da Afirka Dr. Matshidiso Moeti, ya ce wannan wani babban ci gaba ne ga nahiyar Afirka. Yanzu dai yaran da za a haifa a nahiyar, za su rayu ba tare da kwayar cutar ba.

Ofishin WHO mai kula da yankin Afirka dai, ya taya nahiyar Afirka murnar ganin bayan kwayar cutar ta Polio.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China