Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD¡GHarkokin kasuwanci a Afirka sun karkata ga sabbin fasahohi don tunkarar COVID-19
2020-08-26 10:37:58        cri
Wani sabon rahoto da hukumar MDD mai kula da tattalin arzikin Afirka (UNECA) ta fitar, ya nuna cewa, harkokin kasuwancin nahiyar, suna kartata ga sabbin fasahohi na zamani, a wani mataki na rage radadin annobar COVID-19 dake ci gaba da addabar duniya.

Rahoton wanda hukumar UNECA da cibiyar dake nazarin harkokin tattalin arziki ta kasa da kasa suna wallafa cikin hadin gwiwa, shi ne na biyu da aka yi gudanar da bincike game da COVID-19 da tasirin annobar kan tattalin arziki a sassan nahiyar da aka wallafa.

A cewar rahoton, sakamakon binciken ya nuna cewa, manyan kalubaloli guda uku da kamfanonin nahiyar suke fuskanta a yayin da ake fama da annobar, sun hada da raguwar damammaki ta biyan bukatun sabbin masu mu'amula na samun kayayyaki da hidimomi, da karancin kudade a hannun jama'a.

Bugu da kari, rahoton ya nuna cewa, a halin yanzu kamfanoni suna samar da rabin kayayyakin da suka saba samarwa, inda kudaden shigar da suke samu ya rage da kimanin kaso 18 cikin 100 a shekarar 2020, idan aka kwatanta da 2019, baya ga hasashen da ake yi na rage karin kaso 20 cikin 100 na ma'aikata a cikin watannni uku masu zuwa.

Rahoton ya kuma yi nuni da cewa, matakan daidaita ayyuka, sun kara haifarwa sana'oi da kananan da matsakaitan kamfanoni Karin kalubale, musamman wadanda ke kula da kayayyaki, sannan annobar ta fi shafarsu fiye da manyan kamfanoni, musamman wadanda ke ayyukan samar da hidima.

A cewar hukumar ta UNECA, abin da rahoton ya gano shi ne, kaso biyu bisa uku na kamfanoni da aka gudanar da bincike a kansu, ya nuna cewa, sun gano sabbin damammaki, don tunkarar wannan matsala.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China