Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bukaci Amurka da ta dakatar da matakan takala ta fuskar aikin soja
2020-08-26 13:28:22        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar tsaron kasar Sin Wu Qian ya yi jawabi a jiya kan yadda wani jirgin saman Amurka ya kutsa kai cikin yankin atisayen soja da Sin ta hana jiragen wasu kasashe ratsawa ta kai, inda ya ce, matakin na Amurka tamkar talaka ce, kuma Sin tana adawa da kuma nuna matukar rashin jin dadinta ga Amurka.

Wu ya ce, jirgin saman na Amurka samfuri U-2 ya kutsa kai yankin da sojan kasar Sin na PLA dake atisayen wanda ta haramtawa sauran jiragen ketare yin shawagi ba tare da samun izni ba a cikin, matakin ya lahanta atisayen da Sin take yi, kuma ya sabawa ka'idar tsaron teku da sararin sama tsakanin Sin da Amurka da sauran ka'idojin kasa da kasa, kuma mataki zai iya haddasa rashin fahimta har da hadari. A cewarsa, matakin na Amurka tamkar talaka ce. A don haka, kasar Sin tana matukar yin adawa da shi, ta kuma tuntubi Amurka don neman daidaita wannan matsala. Haka kuma, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta daina daukar irin wannan mataki, a maimakon haka ta dauki matakan da suka dace don kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan yankin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China