Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masar ta nanata muhimmancin cimma yarjejeniya tsakanin kasashe uku kan madatsar ruwan Nilu
2020-08-26 13:32:44        cri
Kasar Masar ta nanata cewa, ya dace kasashen nan uku, wato, Masar ita kanta da Habasha da Sudan su cimma yarjejeniya kan dokokin cikewa da fara aiki da babban madatsar ruwan nan ta GERD da Habashan ta gina a kan kogin Nilu da kasashen ke cin gajiya.

Da yake karin haske yayin wani taron jakadun kasashen Afirka da ya gudana a birnin Alkahira kan ci gaba na baya-bayan da aka samu tsakanin kasashen uku kan madatsar ruwan, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Masar mai kula da harkokin Afirka, Hamdi Sanad Loza, ya sake jaddada matsayin kasarsa kan wannan batu.

Taron na yini guda, na zuwa ne bayan da Loza ya gudanar da makamanciyar tattaunwa da jakadun Turai a birnin na Alkahira, don jaddada kudurin kasarsa na ganin an cimma yarjejeniya kan madatsar ruwan.

A 'yan shekarun da suka gabata dai, tattaunawar kasashen uku game da dokoki na cikewa da fara aiki da madatsar ruwan, ba ta haifar da sakamako ba, biyo bayan da fargabar da Masar din ke yi cewa, babbar madatsar ruwan, zai shafi kimanin cubic mita biliyan 55.5 na ruwan da kasar ke cin gajiya duk shekara daga kogin na Nilu.

Kasashen Masar da Sudan dai, sun sha gargadin Habasha game da janye ruwan ba tare da cimma yarjejeniya tsakanin kasashen uku ba.

Ana saran bayan kammala aikin gina babban madatsar ruwan da zai lashe dala biliyan 4, za ta samar da sama da megawatts dubu 6 na hasken wutar lantarki, tare da zama madatsar ruwa mafi girma dake samar da wutar lantarki a Afirka.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China