Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An dasa itatuwa domin hana tashin rairayi
2020-08-26 13:38:23        cri
Kauyen Hatubuqigacha dake gundumar Keyouzhong na birnin Hinggan a yankin Mongoliya ta Gida mai cin gashin kansa, a baya ya yi fama da rairayi, a duk lokacin da iska ta kada, har ma ba a iya ganin kome ba a kan hanya, sai rairayi ta ko ina.

Baijilin Baiyila shi ne mai kula da gandun daji na kauyen, yana kula da fili mai fadi muraba'in mita dubu 200. Ya ce, wadannan itatuwa da aka dasa sun taimaka matuka wajen hana tashin rairayi a garinsu.

Ya kara da cewa, a baya, mutanen kauyensu sun dasa itatuwa, amma, galibinsu sun mutu, sabo da ba a kula da su yadda ya kamata ba. Amma, yanzu, akwai masanan dake kula da itatuwa, kuma sun dasa itatuwa da yawa, an kuma samu sakamako mai kyau!

Cikin 'yan shekarun nan, gundumar Keyouzhong ta tsara manufofin kiwon dabbobi, da suka hada da manufar rage adadin tumaki da kara adadin shanu da sauransu, domin inganta rayuwar mazaunan kauyen. A da, mazauna kauyen kowa yana kiwon tumaki, lamarin da ya bata yankin ciyayi sosai. Shi ya sa, aka ba da tallafin kudi ga masu fama da talauci a kauyen, don su sayi shanu, da raya sana'o'in naman shanu. Yanzu, Baijilin Baiyila da iyalinsa suna kiwon shanu guda 10, abin da ya taimaka musu fita daga kangin talauci. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China