Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yankin musamman na tattalin arziki na Shenzhen ya cika shekaru 40 da kafuwa
2020-08-26 15:53:11        cri

Ranar 26 ga watan Agusta, yankin musamman na tattalin arziki na birnin Shenzhen ya cika shekaru 40 da kafuwa, an samu canje-canje da dama a wannan birni, daga karamin kauye zuwa babban birni na zamani. Kuma, kamfanoni masu jarin waje dake birnin sun ga yadda wannan birnin ya canja, sun kuma ba da gudummawa ga yadda birnin ya cimma muradunsa na samun bunkasuwa.

Kamfanin Chia Tai na kasar Thailand ya zo birnin Shenzhen a shekarar 1979, ya samu "takardar iznin kamfanin zuba jari na ketare a birnin Shenzhen mai lamba 0001", mataimakin shugaban kamfanin, kana jami'in reshen kamfanin Chia Tai dake kasar Sin, Yang Xiaoping ya bayyana cewa, birnin Shenzhen yana samun bunkasuwa cikin sauri, kuma birnin ya bunkasa daga wani karamin kauye zuwa babban birni mai kunshe da yawan al'umma sama da miliyan 10, lamarin da ya kasance abin al'ajabi ga kasashen duniya.

Yanzu haka, akwai rassan kamfanin Chia Tai sama da guda 600 a kasar Sin, jarin da kamfanin ya zuba ya zarce yuan miliyan 120,000. Kwanan baya, kamfanin yana fadada ayyukan zuba jari a kasar Sin. Yang Xiaoping ya ce, kamfanin Chia Tai yana da imani kan bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin.

 

Kuma, dangane da tsokacin da wasu 'yan siyasan kasashen ketare suka yi cewar, wai za su lalata dangantakar ciniki dake tsakaninsu da kasar Sin, Yang Xiaoping ya ce, muradunsu na siyasa ba za su canja dokokin da suka shafi tattalin arziki ba, kasar Sin na da manyan kasuwanni, kamfanoni za su gudanar da ayyukansu bisa dokokin tattalin arziki. (Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China