Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sakataren tsaron Amurka ya sake furta zargin Sin da haifar da barazanar tsaro
2020-08-26 20:33:53        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya maida martani ga kalaman sakataren tsaron Amurka Mark Esper, game da zargin kasar Sin da ya yi na kasancewa barazana ga tsaron kasashen duniya.

Zhao Lijian, wanda ya maida martanin a Larabar nan, yayin taron manema labarai na rana rana da aka saba gudanarwa, ya yi tir da kalaman Mr. Esper, wanda aka rawaito shi cikin wata sanarwa na cewa, a shirye suke su dauki mataki kan kasar Sin.

Zhao Lijian ya ce ko alama, ba wani dalili da zai sa Esper ya furta wadannan kalamai, don haka ya gabatar wa jami'in na Amurka da shawara guda, da kuma bayanai na gaskiya biyu, da kuma wasu tambayoyi uku.

Da fari, Mr. Zhao ya shawarci Mr. Esper, da ya karanta, tare da nazartar cikakken bayani da kasar Sin ta fitar, game da karairayi da kuma kalamai na gaskiya da sakataren wajen Amurka Mike Pompeo ya gabatar kan kasar Sin. Yana mai cewa, akwai shaidu masu tarin yawa dake cikin wancan bayani, wadanda za su iya rusa karairayin da ake yadawa, cewa wai Sin barazana ce ga wasu kasashe.

Zhao Lijian ya kuma gabatar da bayanai biyu: inda ya ce da farko, tun daga shekarar 1990, dakarun sojin kasar Sin sun shiga ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD sama da 20, kana Sin ta tura dakarun ta da yawan su ya haura 40,000 cikin irin wadannan ayyuka, wanda hakan ya sanya kasar zama mafi tura dakarun wanzar da zaman lafiya, tsakanin sauran kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin tsaron MDD.

Abu na biyu kuwa, cikin tarihin shekaru 240 da kafuwar kasar Amurka, shekaru 16 ne kacal kasar ba ta shiga wani yaki ba. Kaza lika adadin kasafin kudin Amurka a fannin aikin soji a shekarar 2019 kadai, ya haura dalar Amurka biliyan 716, adadin da ya kai jimillar na sauran kasashe 9 dake biye da ita a wannan fanni.

Game da tambayoyin da Zhao ya gabatarwa Mr. Esper kuwa, ya ce da farko sanin kowa ne Sin na aiwatar da manufofi ne na tsaron kasa a dukkanin ayyukan ta na soja. Kuma kundin tsarin mulkin JKS, da na kasar baki daya, ya fayyace aniyar kasar na nacewa hanyar neman ci gaba ta lumana, da kaucewa danniya. Shin ko Amurka za ta iya bayyanawa duniya ita ma haka manufofin ta suke?

Tambaya ta biyu kuwa ita ce, wace kasa ce, ke da daruruwan sansanonin soji a dukkanin lungu da sako na duniyar nan, wadda kuma ta yi amfani da su wajen kaddamar da yaki, da hare hare ba bisa ka'ida ba a Iraqi, da Syria, da Libya, da karin wasu kasashen ma, kana ta tura jiragen ta na ruwa da na sama, zuwa yankuna masu nisa da yankin ta domin haddasa yaki?.

Na uku kuma, jami'in ya tambayi Mr. Esper, ko wace kasa ce ke ci gaba da rike tunanin cacar baka, tana ci gaba da karya yarjejeniya, da janye kan ta daga abokan huldar ta, take barazana, da karya ka'idojin kasa da kasa?

Daga nan sai Mr. Zhao ya ce ko shakka babu, wasu daga 'yan siyasar Amurka na iya amsa wadannan tambayoyi, muddin dai suna iya mutunta gaskiya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China