Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping da yankunan musamman na kasar Sin
2020-08-26 21:57:45        cri
A watan Agustan shekarar 1980, gwamnatin kasar Sin ta kafa wasu yankunan musamman na raya tattalin arziki a biranen da suka hada da Shenzhen, da Zhuhai, da Shantou, da kuma Xiamen.

Zuwa shekarar 1985, Xi jinping, shugaban kasar Sin na yanzu, ya zama mataimakin magajin birnin Xiamen, inda ya kwashe shekaru 3 yana aiki a can, tare da jagorantar aikin gyare-gyare a fannin hada-hadar kudi, da tsara wani shirin raya birnin na wasu shekaru 15.

A shekarar 2017, taron shugabannin kasashen kungiyar BRICS ya gudana a birnin Xiamen. Xi Jinping ya halarci taron bisa matsayinsa na shugaban kasar Sin, inda ya ce, " Tun da turbar da muka dauka ta zurfafa gyare-gyare ta yi daidai, to, za mu ci gaba bin wannan turba. "

A shekarar 2012, shugaba Xi ya yi rangadi a Shenzhen da Zhuhai, inda ya nuna niyyar gwamnatin kasar Sin ta ci gaba da yin gyare-gyare a kasar, da kara bude kofarta ga sauran kasashe.

Daga bisani, shugaban ya sake yin rangadi a Shenzhen da Zhuhai, da sauran yankunan musamman na bunkasa tattalin arziki, a shekarar 2018. Daga bisani, zuwa shekarar 2019, kasar Sin ta samar da wani shiri na mai da birnin Shenzhen yankin nuna tsarin gurguzu mai yanayin musamman na kasar Sin.

Bayan wasu shekaru 40, yankunan musamman na kasar Sin za su ci gaba da taka muhimmiyar rawa, a kokarin kasar ta zurfafa gyare-gyarenta, a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al'umma.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China