Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU¡GAnnobar COVID-19 ta kara nuna bukatar Afirka ta fadada albarkatunta
2020-08-27 10:32:31        cri
Hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka (AU) ta sanar a jiya Laraba cewa, annobar COVID-19 dake ci gaba da yaduwa a sassan duniya, ta kara nuna bukatar dake akwai ga nahiyar Afirka ta fadada sassan albarkatunta.

Wannan kira na zuwa ne, a dai-dai lokacin da jami'an haraji da masu tsara manufofi na Afirka, ke tattaunawa yayin wani taro na yini biyu da hukumar ta AU ta shirya daga jiya zuwa yau ta kafar bidiyo. Alkaluman da kungiyar mai mambobi 55 ta fitar na nuna cewa, karuwar GDPn nahiyar da aka yi hasashen zai kai tsakanin kasa da 4.9 cikin 100 da kuma kasa kaso 2.1 cikin 100 a wannan shekara, zai haddasa raguwar da ta kai tsakanin dala biliyan 135 da kuma dala biliyan 204, daga dala triliyan 2.59 kafin bullar COVID-19.

A cewar AU, matsalar annobar COVID-19, ta haddasa matsalar talauci, har ma bankin raya Afirka (AfDB) ya yi hasashen cewa, annobar za ta haddasa hasarar tsakanin dala miliyan 28.2 da kuma dala miliyan 49.2, matakain da zai cusa karin kasashen Afirka cikin kangin talauci.

A bisa la'akari da wannan matsala, kungiyar AU ta ce, ya zama wajibi, masu tsara manufofi na nahiyar, su gaggauta daukar tsauraran matakai kan batutuwan da tasirin annobar COVID-19 ta haifar kan tattalin arzikin Afirka, su kuma nazarci shawarwari da aka gabatar, game da batun harajin cinikayya ta yanar gizo, da illolin da za su iya haifarwa, kan yadda kasashen nahiyar suke tara kudaden haraji .(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China