Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Africa CDC: Kimanin kasashen Afirka 20 ne suka rufe kan iyakokinsu baki daya saboda COVID-19
2020-08-27 10:36:42        cri
Hukumar kandagarki da hana yaduwar cututtuka ta Afirka (Africa CDC) ta sanar a jiya Laraba cewa, yanzu haka kimanin kasashen Afirka 20 ne, suka rufe kan iyakokinsu ba shiga ba fita, saboda tsaron yadda annobar COVID-19 ke yaduwa a nahiyar.

Africa CDC, ta bayyana cewa, baya ga yadda wadannan kasashe suka dauki matakan rufe kan iyakokin nasu, galibin kasashe mambobin kungiyar, sun umarci matafiya daga kasashen da wannan cuta ta fi kamari, da ala tilas su killace kansu.

Sabbin alkaluman da hukumar ta fitar na nuna cewa, ya zuwa jiya Laraba, yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a sassan nahiyar ya haura 1,202,918, kana yawan wadanda cutar ta halaka, ya karu zuwa 28,276, akwai kuma kimanin mutane 931,057 da suka warke daga cutar a sassan nhiyar.

Hukumar ta ce, ya zuwa ranar Talata, wasu kasashen nahiyar 15, sun ba da rahoton sama da mutane 10,000 da suka kamu da cutar ta COVID-19, bayan da cutar ta kara bulla a wasu sassan nahiyar. Sai dai ya zuwa yanzu, akwai kasashen nahiyar 32, da suka ba da rahoton kasa da mutane 5,000 da cutar ta harba.¡]Ibrahim¡^

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China